<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>220</hymn_number>
<title>Ta Wurin Ƙaunar Mai Ceto, Sai Lafiya LW220</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ta wurin ƙaunar Mai Ceto, sai lafiya.
 Ƙauna ba ta sakewa kuwa, sai lafiya.
 Jininsa mai tamani ne, ƙaunarsa har abada ce,
 Idonsa ya tsare mu dai, sai lafiya.

[V2]
 2) Ko da muna shan wahala, sai lafiya.
 Shi ya iya cetonmu duk, sai lafiya.
 Murnarmu daga Uban ce, ladanmu daga Yesu ne,
 Tsarkakewarmu ta Ruhu, sai, lafiya.

[V3]
 3) Bege kuwa ya haskaka mu, sai lafiya.
 Bangaskiya ta ƙarfafa mu, sai lafiya.
 Mun dogara kuwa ga Allah, Yesu ne ke biyan bukata,
 Ko a mace ko a raye, sai lafiya.</lyrics>
</song>